1
Ish 45:3
Littafi Mai Tsarki
HAU
Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare, Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji, Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.
Compare
Explore Ish 45:3
2
Ish 45:2
“Ni kaina zan shirya hanya dominka, Ina baji duwatsu da tuddai. Zan kakkarye ƙyamaren tagulla, In kuma daddatse gagara badau na baƙin ƙarfe.
Explore Ish 45:2
3
Ish 45:5-6
“Ni ne Ubangiji, ba wani Allah sai ni. Zan ba ka irin ƙarfin da kake bukata, Ko da yake kai ba ka san ni ba. Na yi wannan domin dukan waɗanda suke daga wannan bangon duniya zuwa wancan Su sani ni ne Ubangiji, Ba kuwa wani Allah sai ni.
Explore Ish 45:5-6
4
Ish 45:7
Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.
Explore Ish 45:7
5
Ish 45:22
“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.
Explore Ish 45:22
6
Ish 45:1
Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji! Ubangiji ya sa shi ya ci al'ummai, Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna, Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni. Ubangiji ya ce wa Sairus
Explore Ish 45:1
7
Ish 45:23
Abin da na faɗa gaskiya ne, Ba kuwa zai sāke ba. Ni, a dukkan yadda nake, na yi alkawari mai ƙarfi, Kowa da kowa zai zo ya durƙusa a gabana, Ya yi wa'adin zama mai biyayya a gare ni.
Explore Ish 45:23
8
Ish 45:4
Na sa ka domin ka taimaki bawana Isra'ila, Jama'ar da ni na zaɓa. Na ba ka girma mai yawa, Ko da yake kai ba ka san ni ba.
Explore Ish 45:4
Home
Bible
Plans
Videos