1
Ish 1:18
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.
Compare
Explore Ish 1:18
2
Ish 1:19
Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwan da ƙasa take bayarwa.
Explore Ish 1:19
3
Ish 1:17
Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”
Explore Ish 1:17
4
Ish 1:20
Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”
Explore Ish 1:20
5
Ish 1:16
Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta.
Explore Ish 1:16
6
Ish 1:15
“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
Explore Ish 1:15
7
Ish 1:13
Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.
Explore Ish 1:13
8
Ish 1:3
Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama'ata Isra'ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”
Explore Ish 1:3
9
Ish 1:14
Ina ƙin bukukuwanku na amaryar wata, da na tsarkakan ranaku. Sun zama nawaya wadda na gaji da ita.
Explore Ish 1:14
Home
Bible
Plans
Videos