1
Ibr 1:3
Littafi Mai Tsarki
HAU
Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama.
Compare
Explore Ibr 1:3
2
Ibr 1:1-2
A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa, amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya.
Explore Ibr 1:1-2
3
Ibr 1:14
Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?
Explore Ibr 1:14
4
Ibr 1:10-11
Da kuma, “Ya ubangiji, kai ne ka halicci duniya tun farko, Sammai kuma aikinka ne. Su za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufa
Explore Ibr 1:10-11