1
Afi 2:10
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
Compare
Explore Afi 2:10
2
Afi 2:8-9
Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah, ba kuwa saboda da aikin lada ba, kada wani ya yi fariya.
Explore Afi 2:8-9
3
Afi 2:4-5
Amma Allah da yake mai yalwar jinƙai ne, saboda matsananciyar ƙaunar da yake yi mana, ko a sa'ad da muke matattu ma ta wurin laifofinmu, sai ya rayar da mu tare da Almasihu (ta wurin alheri an cece ku)
Explore Afi 2:4-5
4
Afi 2:6
a cikin Almasihu Yesu kuma ya tashe mu tare, har ya ba mu wurin zama tare a samaniya.
Explore Afi 2:6
5
Afi 2:19-20
Wato ashe, ku ba baƙi ba ne kuma, ko kuwa bāre, ai, ku abokan 'yanci ne na tsarkaka, iyalin Allah kuma, waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin
Explore Afi 2:19-20
Home
Bible
Plans
Videos