1
M.Sh 1:30-31
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku. Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.’
Compare
Explore M.Sh 1:30-31
2
M.Sh 1:11
Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!
Explore M.Sh 1:11
3
M.Sh 1:6
“Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.
Explore M.Sh 1:6
4
M.Sh 1:8
Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”
Explore M.Sh 1:8
5
M.Sh 1:17
Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’
Explore M.Sh 1:17