Tun da yake Allah ya yi musu baiwa daidai da wadda ya yi mana, sa'ad da muka gaskata da Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni in dage wa Allah!” Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”