1
2Kor 11:14-15
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ba abin mamaki ba ne kuwa, domin ko Shaiɗan ma da kansa, yakan mai da kansa kamar shi mala'ikan haske ne. Don haka, ba abin mamaki ba ne in bayinsa ma sun mai da kansu kamar su bayi ne na aikin adalci. A ƙarshe za a saka musu gwargwadon ayyukansu.
Compare
Explore 2Kor 11:14-15
2
2Kor 11:3
Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.
Explore 2Kor 11:3
3
2Kor 11:30
In ma lalle ne in yi gadara, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suke nuna raunanata.
Explore 2Kor 11:30