Sai Saul ya yi magana da Jonatan, ɗansa, da dukan fādawansa, cewa yana shiri ya kashe Dawuda. Amma Jonatan ɗan Saul yana jin daɗin Dawuda ƙwarai. Jonatan ya faɗa wa Dawuda ya ce, “Saul, mahaifina, yana so ya kashe ka, domin haka sai ka lura da kanka da safe, ka ɓuya a wani lungu.