1Sam 19:9-10
1Sam 19:9-10 HAU
Ubangiji kuma ya sa mugun ruhu ya sauko kan Saul sa'ad da yake zaune a gidansa, da mashi a hannunsa. Dawuda kuma yana ta kaɗa masa garaya. Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, mashin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere.





