Da Saul ya ji, sai Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai. Ya kwance shanun, ya yanka gunduwa gunduwa, ya aika da su ko'ina a ƙasar Isra'ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Duk wanda bai fito ya bi Saul da Sama'ila ba, to, haka za a yi da shanun nomansa!”
Jama'a suka ji tsoron abin da Ubangiji zai yi, suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.