1
1Kor 13:4-5
Littafi Mai Tsarki
HAU
Ƙauna tana sa haƙuri da kirki. Ƙauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. Ƙauna ba ta sa ɗaga kai ko rashin kārā, ƙauna ba ta sa sonkai, ba ta jin tsokana, ba ta riƙo.
Compare
Explore 1Kor 13:4-5
2
1Kor 13:7
Ƙauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da bangaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali, da jimiri a cikin kowane hali.
Explore 1Kor 13:7
3
1Kor 13:6
Ƙauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya.
Explore 1Kor 13:6
4
1Kor 13:13
To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.
Explore 1Kor 13:13
5
1Kor 13:8
Ƙauna ba ta ƙarewa har abada. Annabci zai shuɗe, harsuna za su ɓace, ilimi kuma zai shafe.
Explore 1Kor 13:8
6
1Kor 13:1
Ko da zan yi magana da harsunan mutane, har da na mala'iku, amma ya zamana ba ni da ƙauna, na zama ƙararrawa mai yawan ƙara ke nan, ko kuwa kuge mai amo.
Explore 1Kor 13:1
7
1Kor 13:2
Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.
Explore 1Kor 13:2
8
1Kor 13:3
Ko da zan sadaukar da duk abin da na mallaka, in kuma ba da jikina a ƙone, in har ba ni da ƙauna, to, ban amfana da kome ba.
Explore 1Kor 13:3
9
1Kor 13:11
Sa'ad da nake yaro, nakan yi magana irin ta ƙuruciya, nakan yi tunani irin na ƙuruciya, nakan ba da hujjojina irin na ƙuruciya. Da na isa mutum kuwa, sai na bar halin ƙuruciya.
Explore 1Kor 13:11