Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa'ad da kuke sha, domin tunawa da ni.” Wato, duk sa'ad da kuke cin gurasar nan, kuke kuma sha a ƙoƙon nan, kuma ayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.