1
Afisawa 6:12
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.
Compare
Explore Afisawa 6:12
2
Afisawa 6:18
A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.
Explore Afisawa 6:18
3
Afisawa 6:11
Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.
Explore Afisawa 6:11
4
Afisawa 6:13
Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.
Explore Afisawa 6:13
5
Afisawa 6:16-17
Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
Explore Afisawa 6:16-17
6
Afisawa 6:14-15
Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.
Explore Afisawa 6:14-15
7
Afisawa 6:10
A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi.
Explore Afisawa 6:10
8
Afisawa 6:2-3
Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
Explore Afisawa 6:2-3
9
Afisawa 6:1
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan.
Explore Afisawa 6:1
Home
Bible
Plans
Videos