1
Afisawa 2:10
Sabon Rai Don Kowa 2020
SRK
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
Compare
Explore Afisawa 2:10
2
Afisawa 2:8-9
Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.
Explore Afisawa 2:8-9
3
Afisawa 2:4-5
Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.
Explore Afisawa 2:4-5
4
Afisawa 2:6
Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.
Explore Afisawa 2:6
5
Afisawa 2:19-20
Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin.
Explore Afisawa 2:19-20