Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.” Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma