YouVersion Logo
Search Icon

Tit 2

2
Koyar da Kyakkyawar Koyarwa
1Amma kai kam, sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa. 2Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri. 3Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu, 4ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da 'ya'yansu, 5su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah. 6Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai. 7Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa, 8da kuma sahihiyar maganar da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zarginmu. 9Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsar da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya, 10ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai, don su ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu ta kowane hali.
11Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane, 12yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah, 13muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, 14#Zab 130.8; Fit 19.5; M.Sh 4.20; 7.6; 14.2; 1Bit 2.9 wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.
15Ka yi ta sanar da waɗannan abubuwa, kana gargaɗar da su, kana tsawatarwa da ƙaƙƙarfan umarni. Kada ka yarda kowa yă raina ka.

Currently Selected:

Tit 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy