Rom 3
3
1To, ina fifikon Bayahude? Ko kuma ina fa'idar kaciya? 2Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah. 3To, ƙaƙa ke nan in waɗansu sun ci amanar nan? Sai cin amanarsu ya shafe cikar alkawarin Allah? 4#Zab 51.4 A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa,
“Don maganarka tă tabbatar da adalcinka,
Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”
5In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.) 6A'a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari'a? 7In kuwa, a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka kara ɗaukaka shi, to, don me har yanzu ake hukunta ni a kan ni mai zunubi ne? 8In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana yanke, cewa haka muke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.
Babu Mai Adalci
9To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A'a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al'ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su. 10#Zab 14.1-3; 53.1-3Kamar yadda yake a rubuce cewa,
“Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,
11Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.
12Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya,
Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”
13 #
Zab 5.9;
Zab 140.3
“Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne,
Maganarsu ta yaudara ce.”
“Masu ciwon baki ne.”
14 #
Zab 10.7
“Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.”
15 #
Ish 59.7,8 “Masu hanzarin zub da jini ne,
16Ta ko'ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki,
17Ba su kuma san hanyar salama ba.”
18 #
Zab 36.1
“Babu tsoron Allah a cikin sha'aninsu sam.”
19To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take. 20#Zab 143.2; Gal 2.16 Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.
Adalci ta Wurin Bangaskiya
21A yanzu, ba kuwa a game da shari'a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa suke yi wa shaida. 22#Gal 2.16 Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci, 23gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah. 24Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi. 25Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar, 26domin a nuna adalcinsa a wannan zamani, wato a bayyana shi kansa mai adalci ne, mai kuɓutar da duk mai gaskatawa da Yesu kuma.
27To, ina kuma fariyarmu ta shiga? Ina kuwa! Ta wace hanya aka kawar da ita? Ta aikin lada? A'a, sai dai ta hanyar bangaskiya. 28Domin mun amince, cewa ta bangaskiya ne mutum yake kuɓuta, ba ta kiyaye ayyukan Shari'a ba. 29Wato Allah, Allahn Yahudawa ne kurum? Ashe, ba na al'ummai ba ne kuma? Hakika na al'ummai ne ma, 30#M.Sh 6.4; Gal 3.20 tun da yake Allah ɗaya ne, zai kuwa kuɓutar da masu kaciya ta wurin bangaskiya, marasa kaciya ma ta wannan bangaskiya. 31Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.
Currently Selected:
Rom 3: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: