Rom 12
12
Hadaya Mai Rai
1Don haka ina roƙonku 'yan'uwa, saboda yawan jinƙai na Allah, ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi. 2Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.
3Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi. 4#1Kor 12.12 Wato kamar yadda gaɓoɓi da yawa suke harhaɗe a jiki ɗaya, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba, 5haka mu ma, ko da yake muna da yawa, jiki ɗaya muke haɗe da Almasihu, kowannenmu kuma gaɓar ɗan'uwansa ne. 6#1Kor 12.4-11 Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu, 7in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa, 8mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara'a.
Gargaɗi a kan Zaman Kirista
9Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari. 10A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa. 11Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji. 12Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a. 13Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.
14 #
Mat 5.44; Luk 6.28 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su. 15Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka. 16#K.Mag 3.7 Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne. 17Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa. 18In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa. 19#M.Sh 32.35 Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.” 20#K.Mag 25.21,22 Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.” 21Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
Currently Selected:
Rom 12: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: