YouVersion Logo
Search Icon

Rom 10

10
1Ya 'yan'uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto. 2Na dai shaida su a kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba. 3Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar. 4Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.
5 # L.Fir 18.5 Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta. 6#M.Sh 30.12-14 Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu. 7Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” Wato yă ta da Almasihu daga matattu. 8Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi. 9Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto. 10Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto. 11#Ish 28.16 Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.” 12Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi. 13#Yow 2.32 “Duk wanda kuwa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”
14Amma ta ƙaƙa za su yi addu'a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa'azi? 15#Ish 52.7 Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!” 16#Ish 53.1 Amma ba duka ne suka yi na'am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?” 17Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.
18 # Zab 19.4 Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji.
“Muryarsu ta gama duniya duka,
Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”
19 # M.Sh 32.21 Har wa yau, ina tambaya. Shin, Isra'ila kam, ba su fahimta ba ne? Da farko dai Musa ya ce,
“Zan sa ku kishin waɗanda ba al'umma ba ne,
Zan kuma sa ku fushi da wata al'ummar marar fahimta.”
20 # Ish 65.1 Ishayan kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce,
“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni.
Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”
21 # Ish 65.2 Amma a game da isra'ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama'a marasa biyayya, masu tsayayya.”

Currently Selected:

Rom 10: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in