Zab 9
9
Godiya ga Allah saboda Adalcinsa
1Zan yabe ka da zuciya ɗaya, ya Ubangiji,
Zan hurta dukan abubuwa masu banmamaki da ka yi.
2Zan raira waƙa da farin ciki sabili da kai,
Zan raira yabo gare ka, ya Maɗaukaki!
3Magabtana sun jā da baya da suka gan ka,
Suka faɗi, suka mutu.
4Kai da kake alƙali mai adalci
Ka zauna a kursiyinka,
Ka kuwa yi shari'ar da ta yi mini daidai.
5Ka kā da arna,
Ka kuma hallakar da mugaye,
Ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba.
6An hallaka abokan gābanmu har abada,
Ka lalatar da biranensu,
An kuma manta da su sarai.
7Amma Ubangiji sarki ne har abada,
Ya kafa kursiyinsa domin yin shari'a.
8Yana mulkin duniya da adalci,
Yana yi wa mutane shari'a da gaskiya.
9Ubangiji mafaka ne ga waɗanda ake zalunta,
Wurin ɓuya a lokatan wahala.
10Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji,
Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.
11Ku yabi Ubangiji, shi da yake mulki a Sihiyona!
Ku faɗa wa kowace al'umma abin da ya yi!
12Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya,
Ba ya mantawa da kukansu,
Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.
13Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai!
Ka dubi irin wulakancin da maƙiya suka yi mini!
Ka kuɓutar da ni daga mutuwa, ya Ubangiji,
14Domin in iya tsayawa a gaban jama'ar Urushalima,
In faɗa musu dukan abin da ya sa nake yabonka.
Zan yi farin ciki saboda ka cece ni.
15Arna sun haƙa rami sun kuwa fāɗa ciki,
Sun ɗana tarko, ya kuwa kama su.
16Ubangiji ya bayyana kansa ta wurin shari'arsa mai adalci,
Mugaye sun kama kansu da abubuwan da suka aikata.
17Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye,
Da dukan waɗanda suke ƙin Allah.
18Ba kullum ne ake ƙyale masu bukata ba,
Ba za a danne sa zuciyar waɗanda ake zalunta ba har abada.
19Ka zo, ya Ubangiji! Kada ka bari mutane su gagare ka!
Ka kawo arna a gabanka, ka hukunta su.
20Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji,
Ka sa su sani su mutane ne kawai.
Currently Selected:
Zab 9: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979