Zab 89
89
Alkawarin Allah da Dawuda
1Ya Ubangiji zan raira waƙar
Madawwamiyar ƙaunarka koyaushe,
Zan yi shelar amincinka a dukan lokaci.
2Na sani ƙaunarka za ta dawwama har abada,
Amincinka kuma tabbatacce ne kamar sararin sama.
3Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa,
Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,
4 #
2Sam 7.12-16; 1Tar 17.11-14; Zab 132.11; A.M 2.30 ‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki,
Zan kiyaye mulkinka har abada.’ ”
5Talikan da suke Sama suna raira waƙa a kan
Abubuwan banmamakin da kake yi,
Suna raira waƙa kan amincinka, ya Ubangiji.
6Ba wani kamarka a Sama, ya Ubangiji,
Ba wani daga su cikin talikai da yake daidai da kai.
7Ana girmama ka a cikin majalisar talikai,
Duk waɗanda suke kewaye da kai suna yin tsoronka ƙwarai.
8Ya Ubangiji Allah, Mai Runduna,
Ba wani mai iko kamarka,
Kai mai aminci ne a kowane abu.
9Kai kake mulkin haukan teku,
Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.
10Ka ragargaza dodon nan Rahab, ka kashe shi,
Da ƙarfin ikonka ka cinye maƙiyanka.
11Duniya taka ce, haka ma samaniya taka ce,
Kai ne ka halicci duniya da dukan abin da yake cikinta.
12Kai ne ka yi kudu da arewa,
Dutsen Tabor da Dutsen Harmon
Suna raira waƙa gare ka don farin ciki.
13Kai kake da iko!
Kai kake da ƙarfi!
14A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka,
Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.
15Masu farin ciki ne jama'ar da suke yi maka sujada, suna raira waƙoƙi,
Waɗanda suke zaune a hasken alherinka.
16Suna murna dukan yini saboda da kai,
Suna kuwa yabonka saboda alherinka.
17Kana sa mu ci babbar nasara,
Da alherinka kakan sa mu yi rinjaye,
18Sabili da ka zaɓar mana mai kāre mu,
Kai, Mai Tsarki na Isra'ila,
Kai ne ka ba mu sarkinmu.
19Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce,
“Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja,
Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama'a.
20 #
1Sam 13.14; A.M 13.22;
1Sam 16.12
Na zaɓi bawana Dawuda,
Na naɗa shi sarkinku.
21Ƙarfina zai kasance tare da shi,
Ikona kuma zai ƙarfafa shi.
22Abokan gābansa ba za su taɓa cin nasara a kansa ba,
Mugaye ba za su kore shi ba.
23Zan ragargaza magabtansa,
In karkashe duk waɗanda suke ƙinsa.
24Zan ƙaunace shi kullum, in amince da shi,
Zan sa ya yi nasara kullayaumin.
25Zan faɗaɗa mulkinsa tun daga Bahar Rum,
Har zuwa Kogin Yufiretis.
26Zai ce mini, ‘Kai ubana ne da Allahna,
Kai ne kake kiyaye ni, kai ne Mai Cetona.’
27 #
W.Yah 1.5
Zan maishe shi ɗan farina,
Mafi girma daga cikin dukan sarakuna.
28Zan riƙa ƙaunarsa har abada,
Alkawarin da na yi da shi kuma zai tabbata har abada.
29A kullayaumin daga cikin zuriyarsa ne za a naɗa sarki,
Mulkinsa zai dawwama kamar sararin sama.
30“Amma idan zuriyarsa sun ƙi yin biyayya da shari'ata,
Ba su kuwa zauna cikin ka'idodina ba,
31In sun ƙyale koyarwata,
Ba su kiyaye umarnaina ba,
32To, sai in hukunta su saboda zunubansu,
Zan bulale su saboda laifofinsu.
33Amma fa, ba zan daina ƙaunar Dawuda ba,
Ba kuwa zan rasa cika alkawarin da na yi masa ba.
34Ba zan keta alkawarin da na yi masa ba,
Ba zan soke ko ɗaya daga cikin alkawaran da na yi masa ba.
35“Da sunana mai tsarki na yi alkawari sau ɗaya tak,
Ba zan yi wa Dawuda ƙarya ba!
36Zuriyarsa za ta kasance kullum,
Zan lura da mulkinsa muddin rana tana haskakawa.
37Zai dawwama kamar wata,
Kamar amintaccen mashaidin nan da yake a sararin sama.”
38Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,
Ka rabu da shi, ka yashe shi.
39Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,
Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.
40Ka rurrushe garun birninsa,
Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.
41Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,
Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.
42Ka ba maƙiyansa nasara,
Ka sa dukansu su yi murna.
43Ka sa makamansa su zama marasa amfani,
Ka bari a ci shi da yaƙi.
44Ka ƙwace masa sandan sarautarsa,
Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.
45Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa,
Ka rufe shi da kunya.
46Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji?
Har abada ne?
Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?
47Ka tuna kwanakin mutum kaɗan ne, ya Ubangiji,
Ka tuna yadda ka halicci mutane duka masu mutuwa ne!
48Wa zai rayu har abada, ba zai mutu ba?
Ƙaƙa mutum zai hana kansa shiga kabari?
49Ya Ubangiji, ina ƙaunarka ta dā?
Ina alkawaran nan waɗanda ka yi wa Dawuda?
50Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka,
Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.
51Ya Ubangiji, kada ka manta da yadda maƙiyanka
suka ci mutuncin zaɓaɓɓen sarki da ka naɗa!
Suka yi ta cin mutuncinsa duk inda ya tafi.
52Mu yabi Ubangiji har abada! Amin! Amin!
Currently Selected:
Zab 89: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979