Zab 81
81
Waƙar Idi
1Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu,
Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!
2A fara waƙa, ku buga bandiri,
Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.
3 #
L.Ƙid 10.10
Ku busa ƙaho domin idin,
A amaryar wata,
Da a tsakiyar farin wata.
4Wannan doka ce a Isra'ila,
Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.
5Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila,
A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar.
Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,
6“Na ɗauke muku kayayyaki masu nauyi da kuke ɗauke da su a kā,
Na sa kuka ajiye kwandunan aikinku.
7 #
Fit 17.7; L.Ƙid 20.13 Sa'ad da kuke shan wahala
Kuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku.
Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku,
Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.
8“Ya kuma jama'ata Isra'ila ku kasa kunne,
Ina kuwa so ku saurara gare ni.
9 #
Fit 20.2,3; M.Sh 5.6,7 Faufau kada ku bauta wa gumaka,
Ko ku yi sujada ga wanina.
10Ni ne Ubangiji Allahnku,
Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.
Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku.
11“Amma jama'ata ba su kasa kunne gare ni ba.
Isra'ila ta ƙi yi mini biyayya.
12Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu,
Su aikata duk irin abin da suka ga dama.
13Ina kuwa so jama'ata su kasa kunne gare ni,
Su kuwa yi mini biyayya!
14Da sai in kori abokan gābansu nan da nan,
In yi nasara da dukan maƙiyansu.
15Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro,
Hukuncinsu na har abada ne.
16Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama,
In ƙosar da ku da zuma.”
Currently Selected:
Zab 81: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979