Bible App logo
Search Icon

Zab 75

75
Allah Ya Ƙasƙantar da Mugaye, Ya Ɗaukaka Adalai
1Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka!
Muna shelar sunanka mai girma,
Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata!
2“Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah,
“Zan kuwa yi shari'ar gaskiya.
3Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace,
Zan ƙarfafa harsashin gininta.
4Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama,
Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya,
5Na dai faɗa musu su daina yanga,
Su daina yin taƙama.”
6Hukunci ba daga gabas, ko yamma,
Ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba.
7Allah yake yin shari'a,
Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu.
8Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo,
Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi,
Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha,
Suka shanye shi ƙaƙaf.
9Amma har abada ba zan daina yin magana a kan Allah na Yakubu ba,
Ko in daina raira yabbai gare shi.
10Shi zai karya ikon mugaye,
Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi.

Currently Selected:

Zab 75: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in