Zab 65
65
Yabo da Miƙa Hadaya ta Godiya
1Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona,
Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.
2Saboda kakan amsa addu'o'i,
Dukan mutane za su zo wurinka.
3Zunubanmu sun kāshe mu,
Amma za ka gafarta zunubanmu.
4Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe su
Su zauna a tsattsarkan wurinka!
Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka,
Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!
5Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu,
Ka kuma cece mu ta wurin aikata al'amuran banmamaki.
Mutane daga ko'ina a duniya,
Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna,
Sun dogara gare ka.
6Ka kakkafa duwatsu ta wurin ikonka,
Ka bayyana ƙarfin ikonka.
7Kakan kwantar da rurin tekuna,
Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa,
Kakan kwantar da tarzomar jama'a.
8Dukan duniya ta tsorata,
Saboda manyan ayyuka da ka aikata.
Ayyukanka sukan kawo sowa ta farin ciki
Daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.
9Kakan nuna kana kulawa da ƙasar,
Ta wurin aiko mata da ruwa.
Ka arzuta ta, ta zama dausayi.
Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba,
Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki,
Abubuwan da ka aikata ke nan.
10Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome,
Ka jiƙe su da ruwa,
Ka tausasa ƙasar da yayyafi,
Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.
11Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka!
Inda ka tafi duka akwai wadata!
12Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba,
Tuddai kuma suna cike da farin ciki.
13Sauruka suna cike da tumaki,
Kwaruruka suna cike da alkama,
Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!
Currently Selected:
Zab 65: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979
Zab 65
65
Yabo da Miƙa Hadaya ta Godiya
1Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona,
Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.
2Saboda kakan amsa addu'o'i,
Dukan mutane za su zo wurinka.
3Zunubanmu sun kāshe mu,
Amma za ka gafarta zunubanmu.
4Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe su
Su zauna a tsattsarkan wurinka!
Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka,
Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!
5Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu,
Ka kuma cece mu ta wurin aikata al'amuran banmamaki.
Mutane daga ko'ina a duniya,
Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna,
Sun dogara gare ka.
6Ka kakkafa duwatsu ta wurin ikonka,
Ka bayyana ƙarfin ikonka.
7Kakan kwantar da rurin tekuna,
Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa,
Kakan kwantar da tarzomar jama'a.
8Dukan duniya ta tsorata,
Saboda manyan ayyuka da ka aikata.
Ayyukanka sukan kawo sowa ta farin ciki
Daga wannan iyakar duniya zuwa wancan.
9Kakan nuna kana kulawa da ƙasar,
Ta wurin aiko mata da ruwa.
Ka arzuta ta, ta zama dausayi.
Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba,
Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki,
Abubuwan da ka aikata ke nan.
10Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome,
Ka jiƙe su da ruwa,
Ka tausasa ƙasar da yayyafi,
Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.
11Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka!
Inda ka tafi duka akwai wadata!
12Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba,
Tuddai kuma suna cike da farin ciki.
13Sauruka suna cike da tumaki,
Kwaruruka suna cike da alkama,
Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!
@Bible Society of Nigeria 1979