Zab 60
60
Addu'ar Neman Taimako
(Zab 108.6-13)
1Ka rabu da mu, ya Allah, har aka ci nasara a kanmu,
Ka yi fushi da mu, amma yanzu sai ka juyo wurinmu!
2Ka sa ƙasar ta girgiza, ka tsaga ta.
Yanzu sai ka warkar da tsaguwarta, gama tana gab da fāɗuwa!
3Ka sa jama'arka su sha wahala ƙwarai,
Ka ba mu ruwan inabin da ya bugar da mu.
4Ka ta da tuta ga masu tsoronka,
Domin su juya su gudu daga abokin gāba.
5Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,
Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.
6A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,
“Da nasara zan raba Shekem,
Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.
7Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,
Ifraimu ne kwalkwalina,
Yahuza kuma sandana ne na sarauta.
8Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,
Edom kuwa kamar akwatin takalmina.
Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”
9Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?
Wa zai kai ni Edom?
10Da gaske ka yashe mu ke nan?
Ba za ka yi tafiya tare da sojojinmu ba?
11Ka taimake mu, mu yaƙi abokan gāba,
Domin taimako irin na mutum banza ne!
12Idan Allah yana wajenmu,
Za mu yi nasara,
Zai kori abokan gābanmu.
Currently Selected:
Zab 60: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979