Bible App logo
Search Icon

Zab 5

5
Addu'ar Neman Tsari daga Mugaye
1Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji,
Ka kuma ji ajiyar zuciyata.
2Ya Sarkina, Allahna,
Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.
3A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji,
Da safe za ka ji muryata,
Da hantsi zan yi addu'ata,
In kuma jira amsa.
4Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne,
Ba ka yarda da mugunta a gabanka.
5Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya,
Kana ƙin mugaye.
6Kakan hallakar da duk maƙaryata,
Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.
7Amma ni, ina iya zuwa wurinka,
Saboda ƙaunarka mai girma,
In yi sujada a tsattsarkan Haikalinka,
In kuma rusuna maka da bangirma.
8Ina da abokan gāba da yawa, ya Ubangiji,
Ka bi da ni in aikata nufinka,
Ka kuma fayyace mini hanyarka domin in bi ta!
9 # Rom 3.13 Abin da maƙiyana ke faɗa,
Ba abin da za a yarda da shi ba ne,
Su dai, so suke su hallakar kawai,
Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake,
Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.
10Ka kāshe su, ka hukunta su, ya Allah
Ka watsar da mugayen shirye-shiryensu,
Ka kore su daga gabanka sabili da yawan zunubansu,
Da kuma tayarwar da suke yi maka.
11Duk waɗanda suka fake gare ka za su yi farin ciki,
Kullum za su yi ta raira waƙa domin murna.
Kana kiyaye waɗanda suke ƙaunarka,
Suna kuwa matuƙar murna saboda kai.
12Ka sa wa masu yi maka biyayya albarka, ya Ubangiji,
Alherinka yana kāre su kamar gārkuwa.

Currently Selected:

Zab 5: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in