Bible App logo
Search Icon

Zab 36

36
Madawwamiyar Ƙaunar Allah
1 # Rom 3.18 Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa,
Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa.
2Domin yana ganin kansa shi wani abu ne,
A tsammaninsa Allah ba zai tona asirinsa ba,
Ya hukunta zunubinsa.
3Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi,
Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.
4Yana ƙulla mugunta lokacin da yake kwance a gadonsa,
Halinsa ba shi da kyau,
Ba ya ƙin abin da yake mugu.
5Madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji,
Ta kai har sammai,
Amincinka ya kai sararin sammai.
6Adalcinka kafaffe ne,
Kamar manyan duwatsu.
Hukuntanka kamar teku mai zurfi suke.
Ya Ubangiji, kai kake lura da mutane da dabbobi.
7Ina misalin darajar madawwamiyar ƙaunarka, ya Ubangiji!
Mutane sukan sami mafaka a ƙarƙashin fikafikanka.
8Sukan yi biki da yalwataccen abincin da yake Haikalinka,
Kakan shayar da su daga koginka na alheri.
9Kai ne mafarin dukan rai,
Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske.
10Ka yi ta ƙaunar waɗanda suka san ka,
Ka yi wa adalai alheri.
11Kada ka bar masu girmankai su fāɗa mini,
Kada ka bar mugaye su kore ni.
12Dubi inda mugaye suka fāɗi!
Can suka kwanta, ba su iya tashi.

Currently Selected:

Zab 36: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in