Zab 26
26
Addu'ar Neman Tsare Mutunci
1Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji,
Gama na yi abin da suke daidai,
Na dogara gare ka gaba ɗaya.
2Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji,
Ka gwada muradina da tunanina.
3Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni,
Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.
4Ba na tarayya da mutanen banza,
Ba abin da ya gama ni da masu riya.
5Ina ƙin tarayya da masu mugunta,
Nakan kauce wa mugaye.
6Ya Ubangiji, na wanke hannuwana
Don in nuna ba ni da laifi,
Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.
7Na raira waƙar godiya,
Na faɗi dukan ayyukanka masu banmamaki.
8Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake,
Inda ɗaukakarka yake zaune.
9Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi,
Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,
10Mutanen da suke aikata mugunta a dukan lokaci,
A koyaushe suna shirye don su ba da rashawa.
11Amma ni, ina yin abin da yake daidai,
Ka yi mini jinƙai ka fanshe ni!
12Na kuɓuta daga dukan hatsarori,
A taron sujada na yabi Ubangiji!
Currently Selected:
Zab 26: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979