Zab 23
23
Ubangiji Makiyayina Ne
1Ubangiji makiyayina ne,
Ba zan rasa kome ba.
2 #
W.Yah 7.17
Yana sa ni in huta a saura mai ɗanyar ciyawa,
Yana bi da ni a tafkuna masu daɗin ruwa, suna kwance lif.
3Yana ba ni sabon ƙarfi.
Yana bi da ni a hanyar da suke daidai kamar yadda ya alkawarta.
4Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa,
Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji,
Gama kana tare da ni!
Sandanka na makiyayi da kerenka
Suna kiyaye lafiyata.
5Ka shirya mini liyafa
Inda maƙiyana duk za su iya ganina,
Ka marabce ni, ka shafe kaina da mai,
Ka cika tanduna fal da mai.
6Hakika, alherinka da ƙaunarka
Za su kasance tare da ni muddin raina.
Haikalinka zai zama gidana har abada.
Currently Selected:
Zab 23: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979