Zab 19
19
Ayyukan Allah da Shari'arsa
1Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah!
Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!
2Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye,
Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da take biye.
3Ba magana ko kalma da aka hurta,
Ba wani amon da aka ji,
4 #
Rom 10.18
Duk da haka muryarsu ta game duniya duka,
Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya.
Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,
5Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa,
Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.
6Takan fara daga wannan ƙarshen sararin sama, ta kewaye zuwa wancan.
Ba abin da zai iya ɓuya daga zafinta.
7Dokar Ubangiji cikakkiya ce,
Tana wartsakar da rai.
Umarnan Ubangiji abin dogara ne,
Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.
8Ka'idodin Ubangiji daidai suke,
Waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi.
Umarnan Ubangiji daidai suke,
Sukan ba da fahimi ga zuciya.
9Daidai ne a bauta wa Ubangiji,
A ci gaba da yi har abada.
Duk abin da Ubangiji ya hukunta daidai ne,
A kullum hukuntan Ubangiji daidai suke.
10Abin da ake so ne fiye da zinariya,
I, fiye da tatacciyar zinariya ma,
Sun fi zuma zaƙi,
I, fiye da tatacciyar zuma ma.
11Suna ba ni ilimi, ni baranka,
Ina samun ladan yin biyayya da su.
12Ba mai iya ganin kuskuren kansa,
Ka cece ni daga ɓoyayyun laifofi!
13Ka tsare ni kuma daga laifofi na fili,
Kada ka bari su mallake ni.
Sa'an nan zan zama kamili,
In kuɓuta daga mugun zunubi.
14Ka sa maganata da tunanina su zama abin karɓa a gare ka,
Ya Ubangiji, Mafakata da Mai Fansata!
Currently Selected:
Zab 19: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979