Bible App logo
Search Icon

Zab 17

17
Addu'ar Neman Tsari daga Azzalumai
1Ka kasa kunne ga roƙona, ni adalin mutum,
Ka lura da kukana na neman taimako!
Ka kasa kunne ga addu'ata,
Gama ni ba mayaudari ba ne.
2Za ka shara'anta shari'ar da za ta gamshe ni,
Saboda ka san abin da yake daidai.
3Ka san zuciyata,
Kakan zo gare ni da dare,
Ka riga ka jarraba ni sarai,
Ba ka kuwa sami mugun nufi a cikina ba.
Na ƙudurta kuma bakina ba zai yi saɓo ba.
4Zancen aikin sauran mutane,
Na yi biyayya ga umarninka
Ban bi hanyar rashin hankali ba.
5Ina tafiya a kan tafarkinka kullum,
Ban kuwa kauce ba.
6Ina addu'a gare ka, ya Allah,
Domin kakan amsa mini,
Don haka ka juyo wurina ka kasa kunne ga maganata.
7Ka bayyana ƙaunarka mai banmamaki,
Ya Mai Ceto,
Muddin muna kusa da kai mun tsira daga maƙiyanmu.
8Ka kiyaye ni kamar yadda ake kiyaye idanu,
Ka ɓoye ni a inuwar fikafikanka,
9Daga hare-hare na mugaye.
Maƙiyana cike da ƙiyayya sun kewaye ni.
10Ba su jin tausayi, suna magana da girmankai,
11Yanzu suna kewaye da ni duk inda na juya,
Suna jira su sami dama su fyaɗa ni ƙasa.
12Kamar zakoki suke nema su yayyage ni kaca-kaca,
Kamar sagarun zakoki suna fakona a wurin ɓuyarsu.
13Ka zo, ya Ubangiji,
Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su!
Ka cece ni da takobinka daga mugaye,
14Ka cece ni daga gare su da ikonka,
Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan,
Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu,
Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su,
Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!
15Zan gan ka domin ni adali ne,
Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.

Currently Selected:

Zab 17: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in