Zab 12
12
Addu'ar Neman Taimako
1Ka cece ni, ya Ubangiji,
Ba sauran mutanen kirki,
Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.
2Dukan mutane suna yi wa juna ƙarya,
Suna ruɗin junansu da yaudara.
3Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru,
Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya!
4Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama,
Ba kuwa wanda zai hana mu.
Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?”
5Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu,
Domin ana zaluntar masu bukata,
Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi.
Zan ba su zaman lafiya da suke nema!”
6Alkawaran Ubangiji abin dogara ne,
Alkawarai ne na ainihi kamar azurfa
Da aka tace har sau bakwai cikin matoya.
7Ka kiyaye lafiyarmu, ya Ubangiji,
Ka kiyaye mu daga irin waɗannan mutane.
8Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga,
Suna ta yabon abin da yake mugunta.
Currently Selected:
Zab 12: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979