K.Mag 3:13-15
K.Mag 3:13-15 HAU
Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi. Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya. Tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani.





