K.Mag 24
24
1Kada ka ji ƙyashin mugaye, kada ka yi ƙoƙarin yin abuta da su. 2Duk tunaninsu na yin mugunta ne, a duk lokacin da suka buɗe bakinsu sai sun cuci wani.
3An gina gidaje a kan harsashin hikima da fahimi. 4Ta wurin ilimi a kan ƙawata ɗakuna da kyawawan kayayyaki masu tamani.
5Mai hikima ƙaƙƙarfa ne, i, mai ilimi yana daɗa ƙarfi. 6Banda wannan ma, dole ne ka shisshirya a natse kafin ka kama yaƙi. Bisa ga shawarwarin da za ka samu ne za ka yi nasara.
7Kalmomi masu hikima sun yi wa wawa zurfin ganewa ƙwarai, ba shi da ta cewa sa'ad da ake magana a kan muhimman abubuwa.
8Idan a ko yaushe shirye-shiryen mugunta kake, za ka yi suna a kan kuta tashin hankali. 9Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama'a suna ƙin mutum mai rainako.
10Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.
11Kada ka ji nauyin ceton wanda ake janye da shi zuwa inda za a kashe shi. 12Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.
13Ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau. Kamar yadda kakin zuma yake da zaƙi a harshenka, 14haka ilimi da hikima suke da amfani ga ranka. Ka same su, a gaba za ka yi farin ciki.
15Kada ka shirya dabarun yi wa amintacce ƙwace, ko ka ƙwace masa gidansa, wannan mugunta ce. 16Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a ko yaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.
17Kada ka yi murna sa'ad da bala'i ya aukar wa maƙiyinka. 18Ubangiji zai sani in kana murna, ba kuwa zai so haka ba, mai yiwuwa ne ba zai hukunta shi ba.
19Kada ka damu saboda mugaye, kada ka yi ƙyashin masu aikata abin da ba daidai ba. 20Gama mugun mutum ba shi da sa zuciya, ba abin da zai sa zuciya a kansa nan gaba.
21Ɗana, ka yi tsoron Ubangiji, ka kuma ji tsoron sarki, kada ka yi harkar kome da mutanen da suka tayar musu. 22Irin waɗannan mutane sukan hallaka farat ɗaya. Ka taɓa yin tunani a kan bala'in da Allah ko sarki sukan aukar?
Waɗansu sauran Karin Magana na Hikima
23Masu hikima kuma sun faɗi waɗannan abu.
Kuskure ne alƙali ya yi son zuciya. 24Idan ya kuɓutar da mugu, kowane mutum da yake a duniya zai la'anta shi ya ƙi shi. 25Alƙalan da suke hukunta wa mai laifi kuwa, za su arzuta, su ji daɗin kyakkyawan suna.
26Amsar gaskiya ita ce alamar abuta ta ainihi.
27Kada ka gina gidanka ka kafa shi, sai ka gyara gonakinka, ka tabbata za ka sami abin zaman gari.
28Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isasshen dalili ba, ko ka faɗi ƙarya a kansa. 29Kada ka ce, “Zan yi masa daidai da yadda ya yi mini, zan rama masa!”
30Na ratsa ta gonakin inabin wani malalaci, dakiki, 31suna cike da ƙayayuwa, ciyayi sun sha kansu, katangar dutse da take kewaye da su ta faɗi. 32Da na dubi wannan, na yi tunani a kansa, ya zamar mini ishara. 33#K.Mag 6.10,11 “Yi ta ruruminka, ci gaba da barcinka, rungume hannuwanka don ka shaƙata.” 34Amma sa'ad da kake ta sharar barci fatara za ta auka maka kamar ƙungiyar 'yan fashi.
Currently Selected:
K.Mag 24: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: