K.Mag 16
16
Karin Magana Zancen Zaman Mutum
1Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce.
2Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji yana auna manufarka.
3Ka roƙi Ubangiji, ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su.
4Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce.
5Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.
6Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.
7Lokacin da ka yi abin da Ubangiji yake so, ka iya mai da maƙiyanka su zama abokai.
8Gara ka sami kaɗan ta hanyar gaskiya, da ka tara abu mai yawa ta hanyar zamba.
9Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne yake bi da kai cikin ayyukanka.
10Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.
11Ubangiji yana son ma'aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai.
12Sarakuna ba za su iya jurewa da mugunta ba, gama adalci yake sa hukuma ta yi ƙarfi.
13Sarki yana so ya ji gaskiya, zai kuwa ƙaunaci mutanen da suke faɗar gaskiya.
14Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.
15Alherin sarki kamar gizagizai ne masu kawo ruwan sama a lokacin bazara, akwai rai a ciki.
16Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa.
17Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka.
18Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa.
19Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali'u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu.
20Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki.
21Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin haziƙancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da daɗi, haka ma rinjayarsa take.
22Hikima maɓuɓɓugar rai ce ga mai hikima, amma ɓata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.
23Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya faɗa yakan yi rinjaye ƙwarai.
24Kalmomi masu daɗi suna kama da zuma, suna da daɗin ɗanɗana, suna kuma da amfani domin lafiyarka.
25 #
K.Mag 14.12
Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.
26Marmarin cin abinci yakan sa ɗan ƙodago ya yi aiki da ƙwazo, domin yana so ya ci ya ƙoshi.
27Mutumin da yake jin daɗin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa ƙuna suke kamar wuta.
28Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai.
29Mutum mai ta da zaune tsaye yakan ruɗi abokansa, ya kai su ga bala'i.
30Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.
31Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci.
32Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
33Mutane sukan jefa kuri'a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.
Currently Selected:
K.Mag 16: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: