K.Mag 12
12
1Mutumin da yake ƙaunar ilimi yakan so a faɗa masa kuskurensa, wauta ce mutum ya ƙi yarda a faɗa masa laifinsa.
2Ubangiji yana murna da mutanen kirki, amma yakan hukunta masu shirya mugunta.
3Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram.
4Matar kirki abar fāriya ce, abar murna ga mijinta, amma idan ta sa shi kunya, ta zama masa kamar ciwo a ƙashinsa.
5Amintattun mutane za su yi maka abin da yake daidai, amma mugaye za su ruɗe ka.
6Maganganun mugaye na kisankai ne, amma kalmomin adalai sukan ceci waɗanda ake neman ransu.
7Mugaye sukan gamu da faɗuwarsu, ba magāda, amma iyalan adalai sukan dawwama.
8Idan kai haziƙi ne, za a yabe ka, amma idan kai dakiki ne, mutane za su raina ka.
9Gara kana talakanka, kana neman abinci, da ka mai da kanka kai wani abu ne, alhali kuwa abin da za ka ci ya fi ƙarfinka.
10Mutumin kirki yakan lura da dabbobinsa, amma mugaye sukan yi wa nasu ƙeta.
11Manomin da yake aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan aikin banza.
12Iyakar abin da mugaye suke so, shi ne su sami muguntar da za su yi, amma adalai suna tsaye daram.
13Maganganun mugun sukan zamar masa tarko, amma amintacce yakan fid da kansa daga cikin wahala.
14Sakayyar mutum ta rataya ne a kan maganarsa da aikinsa, zai sami abin da ya cancance shi.
15Wawa a kullum tsammani yake abin da yake yi daidai ne, amma masu hikima sukan kasa kunne ga shawara.
16Sa'ad da wawa ya hasala, nan da nan kowa zai sani, amma mai la'akari ba zai nuna ya kula ba.
17Sa'ad da ka faɗi gaskiya, ka yi adalci, amma ƙarairayi su ne jagorar aikata rashin adalci.
18Maganganun rashin tunani suke sa rauni mai zurfi kamar saran takobi, amma kalmomin mai hikima sukan warkar da raunuka.
19Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.
20Waɗanda suke shawarta mugunta za a auka musu farat ɗaya, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
21Ba wani mugun abu da zai sami adali, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala.
22Ubangiji yana ƙin maƙaryata, amma yana murna da masu faɗa da cikawa.
23Mai la'akari zai bar wa cikinsa abin da ya sani, amma wawaye sukan yi ta tallar wautarsu.
24Mutum mai mai da hankali ga aikinsa zai sami iko, amma ragwanci zai sa mutum ya zama bawa.
25Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.
26A ko yaushe adalin mutum yakan gwada halinsa, amma mugaye sukan ɓata a hanya.
27Rago ba zai kai ga biyan bukatarsa ba, amma mai ƙwazo zai sami dukiya.
28Adalci hanyar rai ne, amma wauta hanyar mutuwa ce.
Currently Selected:
K.Mag 12: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: