K.Mag 1
1
Amfanin Karin Magana
1 #
1Sar 4.32
Karin maganar Sulemanu, ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila. 2Ga Karin magana da za su taimake ka ka rarrabe da hikima, da kyakkyawar shawara, da fahimtar ma'anar zurfafan karin magana, 3da yadda za ka karɓi koyarwa ta hanyar hikima, da adalci, da gaskiya, da sanin abin da yake daidai. 4Sukan sa marar sani ya zama masani, sukan koya wa samari yadda za su zama masu amfani. 5Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana, 6don su fahimci ɓoyayyiyar ma'anar da take cikin karin magana, da mawuyatan al'amura waɗanda masu hikima suka ƙago.
7 #
Ayu 28.28; Zab 111.10; K.Mag 9.10 In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.
Gargaɗi da Faɗaka
8Ɗana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, ka mai da hankali ga abin da mahaifiyarka take faɗa. 9Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su ƙara maka kyau.
10Ɗana sa'ad da masu zunubi suka jarabce ka, kada ka yarda 11in suka ce maka, “Zo mu tafi mu nemi wani mutum mu kashe, mu je, mu fāɗa wa marasa laifi mu ji daɗi! 12Ba mu damu da ransu da lafiyarsu ba, mu dai mu tafi mu kashe su, mu hallaka su ɗungum. 13Za mu sami dukiya iri iri, mu cika gidajenmu da ganima! 14Ka zo ka haɗa kai da mu, dukanmu kuwa za mu raba abin da muka sato.”
15Ɗana, kada ka gama kanka da irin waɗannan mutane, ka yi nesa da su. 16Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai. 17Ba shi da amfani a kafa tarko a idon tsuntsun da ake so a kama. 18Amma waɗannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu. 19Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana'ar sata.
Hikima Tana Kira
20 #
K.Mag 8.1-3
Ku kasa kunne! Hikima tana kira a tituna da a kasuwoyi. 21Tana kira da ƙarfi a ƙofofin birni, a duk inda mutane suke tattaruwa.
22Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba? 23Ku kasa kunne lokacin da nake tsauta muku, zan ba ku shawara mai kyau, mu yi tarayya cikin ilimina. 24Ina ta kiranku ina gayyatarku ku zo, amma ba ku kula ba, ba ku mai da hankali gare ni ba. 25Kun ƙi bin shawarwarina duka, ba ku yarda in gyara kuskurenku ba. 26Saboda haka, lokacin da kuke shan wahala, zan yi muku dariya. Zan yi muku ba'a lokacin da razana ta auka muku, 27sa'ad da ta zo muku kamar hadiri mai ƙaƙƙarfar iska mai wahalarwa, sa'ad da kuke shan azaba da damuwa. 28Sa'an nan za ku kira gare ni, amma ba za ku same ni ba. Za ku neme ni a ko'ina, amma ba za ku same ni ba. 29Domin ba ku taɓa sanin amfanin ilimi ba, kun ƙi tsoron Ubangiji a kullum. 30Ba ku taɓa yarda da shawarata ba, ko ku yarda in gyara kuskurenku. 31Saboda haka za ku karɓi sakayyarku, ayyukanku za su cuce ku. 32Marasa sani sukan mutu saboda ba su yarda da hikima ba. Wawaye kuwa sukan hallaka saboda rashin kulawarsu. 33Amma duk wanda ya kasa kunne gare ni, zai zauna lafiya. Ba abin da zai same shi, ba abin da zai tsorata shi.”
Currently Selected:
K.Mag 1: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: