YouVersion Logo
Search Icon

L.Ƙid 26

26
Ƙidaya ta Biyu
1 # L.Ƙid 1.1-46 Bayan annobar, sai Ubangiji ya ce wa Musa da Ele'azara, ɗan Haruna, firist, 2“Ku ƙidaya dukan taron jama'ar Isra'ila tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba bisa ga gidajen ubanninsu. Ku ƙidaya duk wanda ya isa zuwa yaƙi a cikin Isra'ilawa.” 3Sai Musa da Ele'azara, firist, suka yi musu magana a filayen Mowab daura da Yariko, suka ce, 4“A ƙidaya mutane tun daga mai shekara ashirin zuwa gaba kamar yadda Ubangiji ya umarta.”
Isra'ilawa waɗanda suka fita daga ƙasar Masar ke nan.
5Ra'ubainu shi ne ɗan fari na Yakubu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, su ne Hanok, da Fallu, 6da Hesruna, da Karmi. 7Waɗannan yawansu ya kai dubu arba'in da uku da ɗari bakwai da talatin (43,730). 8Fallu ya haifi Eliyab. 9'Ya'yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama'ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji. 10Ƙasa kuwa ta buɗe ta haɗiye su tare da Kora. Wuta kuma ta cinye sauran mutanen ƙungiyar, mutum ɗari biyu da hamsin suka mutu. Suka zama abin faɗakarwa. 11Amma 'ya'yan Kora ba su mutu ba.
12'Ya'yan Saminu, maza, bisa ga iyalansu, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, 13da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu. 14Yawansu ya kai mutum dubu ashirin da biyu da ɗari biyu (22,200).
15Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni, 16da Ezbon, da Eri, 17da Arodi, da Areli. 18Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba'in da ɗari biyar (40,500).
19Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, 'ya'yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan'ana). 20Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera, 21da Hesruna, da Hamul. 22Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba'in da shida da ɗari biyar (76,500).
23Kabilar Issaka ke nan bisa ga iyalansu, da Tola, da Fuwa, 24da Yashub, da Shimron. 25Waɗannan su ne iyalan kabilar Issaka. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da huɗu da ɗari uku (64,300).
26Kabilar Zabaluna ke nan bisa ga iyalansu, Sered, da Elon, da Yaleyel. 27Waɗannan su ne iyalan kabilar Zabaluna. Yawansu ya kai mutum dubu sittin da ɗari biyar (60,500).
28Kabilar Yusufu ke nan bisa ga iyalansu, wato Manassa da Ifraimu.
29Kabilar Manassa, su ne Makir ɗan Manassa. Makir ya haifi Gileyad wanda ya zama tushen zuriyar Gileyad. 30'Ya'yan Gileyad, maza su ne Abiyezer, da Helek, 31da Asriyel, da Shekem, 32da Shemida, da Hefer. 33Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza. 34Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700).
35Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat. 36Iyalin Eran suna lasafta kansu, daga zuriyar Shutela ne. 37Waɗannan su ne iyalan kabilar Ifraimu. Yawansu ya kai dubu talatin da biyu da ɗari biyar (32,500).
38Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram, 39da Shuffim, da Huffim. 40Iyalin Adar da na Na'aman suna lasafta kansu, su daga zuriyar Bela ne. 41Waɗannan su ne 'ya'yan Biliyaminu bisa ga iyalansu. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari shida (45,600).
42Waɗannan su ne kabilar Dan bisa ga iyalansu, Hushim. Waɗannan su ne iyalan kabilar Dan. 43Yawansu ya kai dubu sittin da huɗu da ɗari huɗu (64,400).
44Kabilar Ashiru ke nan bisa ga iyalansu, Yimna, da Yishwi, da Beriya. 45Iyalin Beriya kuwa sune Eber, da Malkiyel, suna lasafta kansu a zuriyar Beriya. 46Sunan 'yar Ashiru Sera. 47Waɗannan su ne iyalan kabilar Ashiru. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da uku da ɗari huɗu (53,400).
48Kabilar Naftali ke nan bisa ga iyalansu, Yezeyel, da Guni, 49da Yezer, da Shallum. 50Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari huɗu (45,400).
51Jimillar Isra'ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).
An Raba Ƙasa ta Hanyar Kuri'a
52 # L.Ƙid 34.13; Josh 14.1,2 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, 53“A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila. 54Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta. 55Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a. 56Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a.”
Kabilar Lawi
57Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. 58Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram, 59wanda ya auri Yokabed 'yar Lawi wadda aka haifa masa a Masar. Yokabed ta haifa wa Amram, Haruna, da Musa, da Maryamu, 'yar'uwarsu. 60#L.Ƙid 3.2Haruna yana da 'ya'ya huɗu maza, Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar. 61#L.Fir 10.1,2; L.Ƙid 3.4Amma Nadab da Abihu sun mutu saboda sun miƙa hadaya da haramtacciyar wuta a gaban Ubangiji. 62Mazan da aka ƙidaya daga mai wata guda zuwa gaba sun kai dubu ashirin da dubu uku (23,000). Ba a haɗa jimillarsu tare da ta sauran Isra'ilawa ba, da yake ba a ba su gādo tare da su ba.
Joshuwa da Kalibu kaɗai suka Ragu
63Waɗannan su ne Isra'ilawa waɗanda Musa da Ele'azara, firist, suka ƙidaya a filayen Mowab wajen Kogin Urdun daura da Yariko. 64Amma a cikin waɗannan da aka ƙidaya, ba wanda ya ragu daga Isra'ilawa waɗanda Musa da Haruna, firist, suka ƙidaya a jejin Sinai. 65#L.Ƙid 14.26-35Gama Ubangiji ya riga ya yi magana a kansu, cewa lalle za su mutu a jeji. Ba wani mutumin da ya ragu daga cikinsu, sai dai Kalibu ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.

Currently Selected:

L.Ƙid 26: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in