Mat 22:19-21
Mat 22:19-21 HAU
Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari. Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”





