YouVersion Logo
Search Icon

Ayu 41

41
1 # Zab 74.14; 104.26; Ish 27.1 “Ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kama kifi?
Ko kuma ka iya zarge harshensa da igiya?
2Ka iya sa wa hancinsa asirka?
Ko ka iya huda muƙamuƙinsa da ƙugiya?
3Zai ta yi maka godo?
Zai yi maka magana da tattausar murya?
4Zai ƙulla alkawari da kai,
Cewa zai zama baranka har abada?
5Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu?
Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata?
6'Yan kasuwa za su saye shi?
Za su karkasa shi ga fatake?
7Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna?
Ko kuwa kansa da māsu?
8In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!
9Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi,
Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.
10Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi.
Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana?
11Wa ya ba ni har da zan biya shi?
Dukan abin da yake cikin duniyan nan nawa ne.
12“Ba zan yi shiru a kan zancen gaɓoɓinsa ba,
Ko babban ƙarfinsa, ko kyan ƙirarsa.
13Wa zai iya yaga babbar rigarsa?
Ko kuwa ya kware sulkensa da aka ninka biyu?
14Wa zai iya buɗe leɓunansa?
Gama haƙoransa masu bantsoro ne.
15An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne,
An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.
16Suna haɗe da juna gam,
Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.
17Sun manne da juna har ba su rabuwa.
18Atishawarsa takan walƙata walƙiya,
Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.
19Harsunan wuta kamar jiniya suna fitowa daga bakinsa,
Tartsatsin wuta suna ta fitowa.
20Hayaƙi na fita daga hancinsa
Kamar tururi daga tukunya mai tafasa,
Ko bāgar da ta kama wuta.
21Numfashinsa yakan kunna gawayi,
Harshen wuta yana fita daga bakinsa.
22A wuyansa ƙarfi yake zaune,
Razana tana rausaya a gabansa.
23Namansa yana ninke, manne da juna,
Gama ba ya motsi.
24Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse,
Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.
25Sa'ad da ya miƙe tsaye, ƙarfafa sukan tsorata,
Su yi ta tutturmushe juna.
26Ko an sare shi da takobi,
Ko an nashe shi da māshi ko hargi, ko an jefe shi,
Ba sa yi masa kome.
27Kamar ciyawa baƙin ƙarfe yake a gare shi,
Tagulla ma kamar ruɓaɓɓen itace take.
28Kibiya ba za ta sa ya gudu ba,
Jifar majajjawa a gare shi kamar jifa da tushiyoyi ce.
29A gare shi kulake kamar tushiyoyi ne,
Kwaranniyar karugga takan ba shi dariya.
30Kaifin ƙamborin cikinsa kamar tsingaro ne.
Yana jan ciki a cikin laka kamar lular ƙarfe.
31Yakansa zurfafa su tafasa kamar tukunya,
Teku kuwa kamar kwalabar man shafawarsa.
32Idan yana wucewa sai a ga hasken dārewar ruwa,
Yakansa zurfafa su yi kumfa.
33A duniya ba kamarsa,
Taliki ne wanda ba shi da tsoro.
34Yakan dubi kowane abu da yake mai alfarma,
Shi sarki ne a bisa dukan masu girmankai.”

Currently Selected:

Ayu 41: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy