Bible App logo
Search Icon

Ayu 24

24
Ayuba Ya Yi Kuka da Yake Allah Bai Kula da Mugunta Ba
1“Me ya sa Allah bai tsai da ranar da zai yi shari'a ba?
Me ya sa ba ya tsai da ranar adalci ga
Waɗanda suka bauta masa?
2“Mugaye sukan ci iyaka,
Don su ƙara yawan gonarsu.
Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.
3Sukan saci jakunan marayu,
Su kama san gwauruwa,
Su ce sai ta biya basusuwanta.
4Sukan hana matalauta samun halaliyarsu,
Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.
5Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji,
Haka matalauta suke,
Ba inda za su iya samo wa 'ya'yansu abinci.
6Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba,
Su tattara 'ya'yan inabi daga gonakin mugaye.
7Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa,
Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.
8Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu.
Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.
9“Mugaye sukan bautar da yara marayu,
Sukan kama 'ya'ya matalauta a bakin bashin da suke bi.
10Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura.
Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.
11Suna matse mai daga 'ya'yan zaitun.
Suna kuma matse ruwan inabi daga 'ya'yan inabi,
Amma su kansu suna fama da ƙishi.
12Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni da
Waɗanda suke baƙin mutuwa a birni,
Amma Allah bai kula da addu'o'insu ba.
13“Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,
Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.
14Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,
Da dare kuma ya yi fashi.
15Mazinaci yakan jira sai da magariba,
Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.
16Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,
Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.
17Gama tsananin duhu kamar safiya yake gare su,
Sun saba da razanar duhu.
18“Rigyawa takan ci mugun mutum,
Ƙasar da ya mallaka kuwa tana ƙarƙashin la'anar Allah.
Ba ya kuma iya zuwa aiki a gonar inabinsa.
19Kamar dusar ƙanƙara take a lokacin zafi da a lokacin fari,
Haka mai zunubi yakan shuɗe daga ƙasar masu rai.
20Ba wanda zai tuna da shi,
mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba.
Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai.
Za a sare mugunta kamar itace.
21Haka yake samun wanda ya wulakanta gwauraye.
Bai kuma nuna alheri ga matan da ba su haihu ba.
22Allah, da ikonsa, yakan hallaka masu ƙarfi,
Allah yakan aikata, sai mugun mutum ya mutu.
23Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya,
Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.
24Mugun mutum yakan ci nasara ɗan lokaci,
Daga nan sai ya yi yaushi kamar tsiro,
Ya yi yaushi kamar karan dawa da aka yanke.
25Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne?
Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”

Currently Selected:

Ayu 24: HAU

Highlight

Copy

Compare

Share

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in