Ayu 22
22
Elifaz ya Zargi Ayuba a kan Aikata Mugunta
1 #
Ayu 35.6-8
Elifaz ya yi magana.
2“Akwai wani mutum, ko mafi hikima,
Wanda zai amfani Allah?
3Gaskiyar da kake yi za ta amfani Allah?
Ko kuwa abin kirki da kake yi zai taimake shi?
4Ai, ba don tsoron Allah da kake yi ba ne,
Ya sa wannan tsautawa da jarrabawa suka same ka.
5Ko kusa ba haka ba ne,
Amma saboda zunubi mai yawa da ka yi ne.
Saboda kuma dukan muguntar da ka aikata.
6Don ka sa ɗan'uwanka ya biya ka bashin da kake binsa,
Ka ƙwace tufafinsa, ka bar shi huntu.
7Ka hana wa waɗanda suke ji ƙishi ruwan sha,
Ka hana waɗanda suke jin yunwa abinci.
8Ka mori ikonka da matsayinka,
Don ka mallaki dukan ƙasar.
9Ba ƙin taimako kaɗai ka yi ba,
Amma har marayu ma ka yi musu ƙwace, ka wulakanta su.
10Don haka ne yanzu akwai ramummuka ko'ina kewaye da kai,
Tsoro ya kama ka nan da nan.
11An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,
Rigyawa ta sha kanka.
12“Ashe, ba a can saman sammai Allah yake zaune ba?
Sai ya sunkuya ya dubi taurari, ko da yake suna can sama ne.
13Duk da haka ka ce, ‘Allah bai san kome ba.
Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari'a?’
14Kana tsammani gizagizai masu duhu sun hana shi gani,
A lokacin da yake tafiya a kan iyakar da take tsakanin duniya da sararin sama.
15“Ka ɗauka a ranka ka bi gurbin da mugaye suke bi kullum?
16Kafin ma su kai ga kwanakinsu,
Sai rigyawa ta shafe su.
17Su ne mutanen da suka ƙi Allah,
Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,
18Ko da yake Allah ne ya arzuta su.
Ba na iya gane tunanin mugaye.
19Mutanen kirki suna murna,
Marasa laifi kuma suna dariya
Sa'ad da suka ga ana hukunta mugaye.
20Duk abin da mugu ya mallaka ya hallaka,
Wuta kuwa ta lashe kowane abu da ya ragu.
21“Yanzu fa, Ayuba, sai ka yi sulhu da Allah,
Ka daina ɗaukarsa kamar maƙiyinka,
In ka yi haka, to, za ka sami albarka.
22Ka karɓi koyarwar da yake yi,
Ka riƙe kalmominsa a zuciyarka.
23Hakika sai ka yi tawali'u, ka koma wurin Allah,
Ka kawar da dukan muguntar da ake yi a gidanka.
24Ka jefar da zinariyarka, zinariyarka mafi kyau,
Ka jefar da ita kamar dutse ko ƙura.
25Bari Allah Mai Iko Dukka ya zama zinariyarka,
Ya zama azurfa, wadda aka tula dominka.
26Sa'an nan za ka dogara ga Allah kullayaumin,
Ka kuma tarar shi ne asalin farin cikinka.
27Sa'ad da ka yi addu'a zai amsa maka,
Za ka kuwa kiyaye alkawaran da ka yi.
28Za ka yi nasara a kowane abu da za ka yi,
Haske kuma zai haskaka hanyarka.
29Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai,
Yakan ceci mai tawali'u.
30Zai ceci wanda yake da laifi,
Idan abin da kake yi daidai ne.”
Currently Selected:
Ayu 22: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

:
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979