Ayu 2:9-10
Ayu 2:9-10 HAU
Sai matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana da amincin nan naka? Don me ba za ka zagi Allah ka mutu ba?” Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na'am da shi, to, me zai sa sa'ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.





