Irm 47:1-2
Irm 47:1-2 HAU
Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa. Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da yake ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da yake cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.

