Irm 44:16-17
Irm 44:16-17 HAU
“Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba! Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.



