Irm 43
43
Tafiya zuwa Masar
1Sa'ad da Irmiya ya gama faɗa wa dukan jama'a maganar da Ubangiji Allahnsu ya aiko musu da ita, 2sai Yazaniya ɗan Hoshaiya, da Yohenan ɗan Kareya, da dukan 'yan tsagera, suka ce wa Irmiya, “Ƙarya kake yi, Ubangiji Allahnmu bai aiko ka da cewa kada mu tafi, mu zauna a Masar ba! 3Amma Baruk ɗan Neriya shi ne ya sa ka faɗi wannan magana gāba da mu, don ka bashe mu a hannun Kaldiyawa domin su kashe mu, ko kuwa su kai mu bauta a Babila.” 4Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji, da dukan jama'a, ba su yi biyayya da umarnin Ubangiji, su zauna a ƙasar Yahuza ba. 5#2Sar 25.26 Amma Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji suka kwashe sauran mutanen Yahuza duka waɗanda suka komo suka zauna a ƙasar Yahuza, daga wurin al'ummai, inda aka kora su, 6mata, da maza, da yara, da gimbiyoyi, da kowane mutum da Nebuzaradan shugaban matsara ya bar wa Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, da annabi Irmiya, da Baruk ɗan Neriya. 7Suka zo ƙasar Masar, gama ba su yi biyayya da muryar Ubangiji ba. Suka sauka a Tafanes.
8Ubangiji kuwa ya yi magana da Irmiya a Tafanes ya ce, 9“Kwashi manyan duwatsu da hannunka, ka ɓoye su a ƙofar shiga fādar Fir'auna a Tafanes a idon mutanen Yahuza, 10ka kuma ce musu, ‘In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ga shi, zan aika wa bawana Nebukadnezzar ya zo ya kafa kursiyin sarautarsa a kan duwatsun nan waɗanda na ɓoye. Zai buɗe babbar alfarwarsa a wurin. 11Nebukadnezzar zai zo ya buga ƙasar Masar. Zai ba annoba waɗanda aka ƙaddara su ga annoba, waɗanda aka ƙaddara ga bauta, za a kai su bauta. Waɗanda aka ƙaddara ga takobi, za su mutu ta takobi. 12Zai cinna wa gidajen gumakan Masar wuta, zai ƙone su, ya tafi da waɗansu, zai tsabtace ƙasar Masar kamar yadda makiyayi yakan kakkaɓe ƙwarƙwata daga cikin tufafinsa, zai kuwa tashi daga wurin lafiya. 13Zai kuma farfashe al'amudan duwatsu na On a ƙasar Masar. Zai ƙone gidajen gumakan Masar da wuta.’ ”
Currently Selected:
Irm 43: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: