Irm 41
41
1 #
2Sar 25.25
A watan bakwai sai Isma'ilu ɗan Netaniya, ɗan Elishama, na cikin zuriyar sarauta, ɗaya daga cikin ma'aikatan sarki, ya zo a wurin Gedaliya ɗan Ahikam a Mizfa tare da mutum goma. Sa'ad da suke cin abinci tare a Mizfa, 2Isma'ilu ɗan Netaniya, da mutanen nan goma da take tare da shi, suka tashi suka sare Gedaliya ɗan Ahikam ɗan shafan, da takobi, suka kashe shi, wato Gedaliya wanda Sarkin Babila ya naɗa ya zama mai mulkin ƙasar. 3Isma'ilu kuma ya kashe dukan Yahudawa da suke tare da Gedaliya a Mizfa da waɗansu sojojin Kaldiyawa da suke a wurin.
4Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani, 5sai waɗansu mutane, su tamanin, suka zo daga Shekem, da Shilo, da Samariya, da gemunsu a aske, da tufafinsu a kece, da jikunansu a tsage. Suka kawo hadaya ta gari da hadayar turare domin su miƙa a Haikalin Ubangiji. 6Sai Isma'ilu ɗan Netaniya ya fito daga cikin Mizfa yana kuka, don ya tarye su. Da ya sadu da su, sai ya ce musu, “Ku zo mu tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam!” 7Sa'ad da suka shiga birnin, sai Isma'ila ɗan Nataniya da mutanen da suke tare da shi suka kashe su, suka jefa su a wata rijiya.
8Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma'ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha'ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba. 9Rijiyar da Isma'ilu ya zuba dukan gawawwakin mutanen da ya kashe mai zurfi ce, sarki Asa ne ya haƙa saboda tsoron Ba'asha Sarkin Isra'ila. Isma'ilu ɗan Netaniya kuwa ya cika ta da gawawwakin mutanen da ya kashe. 10Sai Isma'ilu ya kwashe dukan sauran mutanen da suke Mizfa, gimbiyoyi da dukan jama'ar da aka bari a Mizfa, waɗanda Nebuzaradan, shugaban matsara, ya bari a hannun Gedaliya ɗan Ahikam. Isma'ilu ɗan Netaniya ya kwashe su ganima, ya haye da su zuwa yankin Ammonawa.
11Amma sa'ad da Yohenan ɗan Kareya, tare da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi suka ji irin wannan mugun aiki wanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya yi, 12sai suka kwashe mutanensu duka, suka tafi su yi yaƙi da Isma'ilu ɗan Netaniya. Suka iske shi a babban tafkin da take a Gibeyon. 13Sa'ad da dukan jama'ar da Isma'ilu ya kwashe suka ga Yohenan ɗan Kareya, da dukan shugabannin sojoji tare da shi, sai suka yi murna. 14Dukan mutanen nan da Isma'ilu ya kwashe su ganima daga Mizfa, suka juya, suka koma wurin Yohenan ɗan Kareya. 15Amma Isma'ilu ɗan Netaniya tare da mutum takwas suka tsere suka gudu zuwa wurin Ammonawa.
16Sai Yohenan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji da suke tare da shi, suka kwashe dukan sauran jama'a, waɗanda Isma'ilu ɗan Netaniya ya kamo daga Mizfa bayan ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam, wato sojoji da mata, da yara, da bābāni, su ne Yohenan ya komo da su daga Gibeyon. 17Suka fa tafi suka zauna a wurin Kimham kusa da Baitalami. Suna nufin su tafi Masar, 18don gudun Kaldiyawa, gama suna jin tsoronsu, domin Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam wanda Sarkin Babila ya naɗa shi mai mulkin ƙasa.
Currently Selected:
Irm 41: HAU
Highlight
Copy
Compare
Share
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979

: