YouVersion Logo
Search Icon

L.Mah 7

7
Gidiyon ya Ci Madayanawa
1Sai Yerubba'al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin.
2Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra'ilawa su yi mini fāriya, su ce, ‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.’ 3#M.Sh 20.8 Yanzu sai ka ce wa mutanen, ‘Duk mai jin tsoro da mai rawar jiki, ya koma gida!’ ” Da Gidiyon ya gwada su, mutum dubu ashirin da biyu (22,000) suka koma, dubu goma (10,000) suka tsaya.
4Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai su bakin rafi domin in jarraba maka su a can. Wanda na faɗa maka shi zai tafi tare da kai, to, shi ne zai tafi, wanda kuma na faɗa ba zai tafi tare da kai ba, to, ba zai tafi ba.” 5Gidiyon ya kai mutanen bakin rafi, Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Duk wanda ya tanɗi ruwa kamar kare, sai ka ware shi waje ɗaya. Wanda kuma ya durƙusa ya sha ruwa, ka ware shi waje ɗaya.” 6Yawan waɗanda suka tanɗi ruwa su ɗari uku ne. Sauran mutane duka kuwa sun durƙusa ne suka sha ruwan. 7Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa zan cece ku. Zan ba da Madayanawa a gare ku, ka sallami sauran, kowa ya koma gidansa.” 8Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin.
9A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka. 10Amma idan kana jin tsoro ka tafi kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka. 11Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba. 12Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.
13Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”
14Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba'isra'ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!”
15Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.” 16Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun. 17Sa'an nan ya ce musu, “Sa'ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka. 18Sa'ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoni, sai ku kuma ku busa ƙahonin a kowane gefen sansani, sa'an nan ku yi ihu, ku ce, ‘Ubangiji da Gidiyon!’ ”
19Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu. 20Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!” 21Kowannensu ya yi tsaye a inda yake kewaye da sansanin. Dukan rundunar Madayanawa kuwa suka gudu, suna ihu. 22Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat.
23Jama'ar kabilar Naftali, da Ashiru, da Manassa, suka ji kira, suka fito, suka runtumi Madayanawa. 24Gidiyon kuma ya aika a dukan ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce musu, “Ku gangaro, ku yaƙi Madayanawa, ku tare mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.” Aka kuwa kira dukan Ifraimawa, su kuwa suka hana wa Madayanawa mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara. 25Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.

Currently Selected:

L.Mah 7: HAU

Highlight

Share

Compare

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in