L.Mah 7:5-6
L.Mah 7:5-6 HAU
Gidiyon ya kai mutanen bakin rafi, Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Duk wanda ya tanɗi ruwa kamar kare, sai ka ware shi waje ɗaya. Wanda kuma ya durƙusa ya sha ruwa, ka ware shi waje ɗaya.” Yawan waɗanda suka tanɗi ruwa su ɗari uku ne. Sauran mutane duka kuwa sun durƙusa ne suka sha ruwan.





