Ish 58:4-5
Ish 58:4-5 HAU
Duba, kuna azumi don ku yi jayayya ne, ku yi ta faɗa, ku yi ta naushin juna. Irin wannan azumi naku a wannan rana, ba zai sa a ji muryarku a can Sama ba. Irin azumin da nake so ke nan ne? Wato ranar da mutum zai ƙasƙantar da kansa kawai. Wato ku sunkuyar da kanku ne kamar jema, ku kuma shimfiɗa tsumma, ku barbaɗa toka a inda kuke zama. Kun iya ce da wannan azumi, karɓaɓɓiyar rana ga Ubangiji?





